Masu zanga-zangar da suka bayyana a daidai lokacin da jama’a ke makokin wadanda suka mutu a harin da aka kai na filin jirgin saman Brussels a makon da ya gabata.
‘Yan zanga-zangar da akewa lakabi da Right-wing, sun bayyana suna rera wakokin kin jinin karbar bakin ketare, da alamta sarawar ko kamewa irin ta ‘yan Nazi.
Wani Mai Sana’ar yin gidaje Monique Starck yace, “sun saba bayyana da wannan sigar ta sake dagula lamari, matukar akwai wani babban al’amari makamancin haka a kasa”.
Tun dai faruwar lamarin da ya hallaka akalla mutane 28, jama’a suke wannan dandali don nuna jimami ga mamatan da abin ya ritsa da su.
Wadannan mutane da ke da’awar cewa su ‘yan tsiraru ne masu adawa da ta’addanci, suna isowa sai naushe-naushe tsakaninsu da masu makokin.