‘Yan sanda Birtaniya sun ce sun kama wani mutum dan shekara 23 a yau Litinin wanda ake zargin yana da alaka da mummunan harin da aka kai a wajen wani taron rawa a Manchester, wanda hakan ya kai adadin mutanen da aka kama zuwa 14, wadanda ake zargin suna da hanu a harin.
Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Manchester, ta fitar a yau Litinin ta nuna cewa an kai samamen kama mutumin ne a yankin Shoreham dake gabar ruwa, bayan da aka zarge shi da aikata wasu laifuka da ba su da nasaba da ayyukan ta’addanci.
Wata sanarwa ta daban har ila yau, ta bayyana kama wasu mutane biyu a ranar Lahadi, wanda ya hada da wani mutum mai shekaru 25 a yankin Old Trafford da kuma wani mai shekaru 19 da aka kama a yankin Gorton.
Harin na Manchester an kai shi ne ranar 22 ga watan nan na Mayu, jim kadan bayan da aka fito daga wani taron rawa da wata mawakiyar Amirka Ariana Grande ta shirya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 22 kana ya jikkata wasu sama da 100.