Dan kasuwan Alhaji Dankani Mai Tireda Jega yayi fice a wurin taimakawa jama'a kwarai da gasken gaske.
'Yan fashin sun kai masa hari ne a daren Asabar da ya gabata. 'Yan fashin sun kasheshi har lahira lamarin da ya tunzura jama'ar garin wadanda suka zargi 'yansandan da kin tabuka komi. Sabili da zargin suka shiga zanga zanga da kone kone tare da tunkarar ofishin 'yansandan.
Shaidun gani da ido sun ce akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a arangamar yayin da wasu ashirin da biyar suka jikata.
Sarkin Kebbi ya basu hakuri yace bai kamata ana yin zanga zanga ba da wani tashin hankali game da abun da ya wakana. Masu zanga zanga sun yi kone kone tare da tasar ma oafishin 'yansanda da nufin koneshi. Da karfi sai su 'yansandan suka yunkuro har suka harbe mutane hudu da wata mahaukaciya har lahira.
Rundunar 'yansandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kwamishanan 'yansanda Isiyaku Bara'u yayi bayani inda yace bai san dalilin da yasa masu zanga zangar suka tasarwa ofishin 'yansanda ba har kona barikokinsu guda biyu. Sun kira gwamna ya sa kwamitin bincike domin sun samu labarin siri da ya nuna wasu mutanen garin basa kaunar DPO din garin saboda wasu dalilai nasu.
Jama'ar gari suna zargin 'yansandan da kin kawo doki a lokacin da barayin suke fashi da makamai a gidan marigayin kodayake kwamishanan 'yansandan ya karyata zargin.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5