Al’ummar wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba a arewa maso gabashin Najeriya, sun fara kokawa tare da yin kira ga gwamnati da a kai musu dauki sakamakon ambaliyar ruwan da suka fara fuskanta.
Dama a baya hukumar kula da yanayi ta Najeriya wato NIMET da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA, sun yi gargadin cewa a bana ta yiwu a samu mummunan ambaliyar ruwa da ka iya yin ta'adi matuka.
Wasu mazauna garin Yola, babban birnin jihar Adamawa da kuma wasu mazauna karamar hukumar Lau a Jihar Taraba sun fara fuskantar ambaliyar.
A cikin hirar shi da Sashen Hausa,Mr. Kenneth, wani shugaba a kasuwar katako ta garin Yola, ya ce wannan ambaliyar ruwan da aka fara samu ta yi masu barna, ya kuma alakanta lamarin da toshe magudanan ruwa da akan yi.
A nashi bayanin, Adamu Zubairu, wani mazaunin yankin ya ce sun saba ganin ambaliyar ruwa amma ta bana ta zo musu da ba-zata. Ya kuma yi kira da gwamnati da ta kawo musu dauki.
Mr. Midala Iliya Anuhu, jami'in hukumar bada agajin NEMA, mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, ya ce tun bayan sanarwar gargadin da suka samu daga kwararru suka fara jan hankalin jama’a musamman ganin cewa hasashen da aka yi a bana ya nuna ta yiwu lamarin ya yi muni.
Saurari rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5