Yankin Arewa Maso Gabas Na Gab da Fadawa cikin Yunwa - MDD

'Yan gudun hijira a Adamawa

Biyo bayan kukan da hukumar samar da abinci ta duniya tayi saboda karancin kudin samar ma arewa maso gabas abinci, Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD tace idan ba'a samu kudi kimanin dalar Amurka miliyan 250 ba, nan da 'yan watanni yunwa zata tagayyara dubun dubatan mutane a yankin

Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD ta bada gargadin ne bayan da hukumar samar da abinci ta fito karara ta bayyana cewa mutane fiye da rabin miliyan yunwa zata tagayyarar dasu sanadiyar karancin abincin da bata da kudin saya masu.

Hukumar na bukatar zunzurutun kudi kimanin dalar Amurka miliyan 250 domin shawo kan lamarin nan da 'yan watanni.

A jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da suka fada cikin bala'in rikicin Boko Haram, kodayake wasu sun fara komawa kauyukansu da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram din, da alama tsugune bata kare masu ba.Maza dake komawa basu da aikin yi kuma ba zasu samu su yi noma ba domin rashin tabbacin cikakken tsaro.

Wasu da suka fito daga Gwozah sun ce basu da masauki saboda haka komawa zai yi musu wuya domin basu da abincin da zasu ci, babu kuma wurin noma. Shiga daji ko kewayen gari zuwa noma ma bai taso ba domin tsaro..

Mr. Adamu Kamale dan majlisar wakilai dake wakiltar Michika da Madagali ya bayyana irin halin da mutane ke ciki. Yace mutane na komawa amma suna dari dari saboda yawancin kauyukansu dake kewayen dajin Sambisa mutane basu iya fita su je suyi noma kamar da. Yace damina ta karato amma mutane ba zasu iya zuwa gonakinsu ba saboda har yanzu mayakan Boko Haram suna cikin dajin daram dam.

Ga cikakken bayani daga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Yankin Arewa Maso Gabas Na Gap da Fadawa cikin Yunwa - MDD - 5' 20"