Bayanai na nuna cewa jami'an tsaro kimanin 11 ne 'yanbindigan suka hallaka tare da kone motoci hudu kafin su arce da motoci bakwai.
So saidai a wani karin bayani da yayi dan majalisar dokokin kasa daga yankin Walam Karimu Bureima ya musanta yawan wadanda aka kashe. Injishi mutane hudu aka kashe kana 13 suka ji rauni. Yace sun arce da motoci shida bayan da suka kone motoci hudu.
Ya tabbatar cewa maharan daga kasar Mali suka fito. Yace mutanen yankin na cikin tashin hankali da dimuwa saboda 'yanbindiga sun sha kai hari yankin.
Wata majiya daga hukumomin Nijar ta tabbatar da faruwa wannan al'amarin yayinda ma'aikatar tsaron kasar tace ana cigaba da tattara bayanai. Idan sun gama zasu yiwa manema labarai karin haske.
Tuni dai 'yan kasar Nijar suka fara korafi akan halin tabarbarewar tsaro akan iyaka da kasar Mali. Dabaji Samala shugaban kare hakkin jama'a yace turawan kasashen turai da suke kasarsu ta Nijar su fita su bar masu kasarsu. Yace akan iyakar kasar sai su sojoji baki sun yadda ake barin ko dan kasa ma ya shiga kasarsa.
Ko a ranar takwas ga watan Nuwamban bara wani hari da aka kai a kauyen Banibangu a jihar Walam ta yankin Tillabery ya hallaka sojojin kasar biyu saboda haka Alhaji Salisa Ahmadu ke ganin gwamnatin Nijar ta hanzarta daukan kwararan matakai.
Malam Bello Usman wani makiyayai dake karkarar Abala Tilinge wanda kuma 'yan takife suka taba sare masa hannunsa na hagu na cewa idan abu ya dade da wuya a shawo kansa. Yace wannan abu ya fi shekaru 20 yana aukuwa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5