WASHINGTON, DC —
Shugaban kungiyar 'yanbangan Najeriya Alhaji Ali Sokoto yace sun san 'yanfashin dake yiwa wasu sassan jihohin Zamfara da Sokoto da Katsinada Kaduna barazana.
Alhaji Ali Sokoto shugaban kungiyar 'yanbangan Najeriya yace sun san 'yanfashin dake damun jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna kuma zasu iya tunkararsu idan aka taimakesu da kayan aiki. Yace jami'ansa nada kwarin gwiwar tunkarar duk wani bata gari da ya damu jama'a idan har gwamnati zata basu gudunmawar da ta dace.
Yayin da yake yin jawabi Alhaji Ali yace suna neman tallafi kama abun da ya fara daga gwamnatin tarayya har zuwa na kananan hukumomi. Yace idan an basu gudummawa ana kuma taimakawa 'ya'yan kungiyar a koina za'a samu zaman lafiya. Yace wadanda suke fashin 'yan kasa ne ba baki ba ne kuma an sansu. To amma saboda rashin kula daga gwamnati shi ya sa lamarin yayi tsamari.
Suna bukatan taimako da motoci da kudade. Shugaban yace idan an basu kaya irin na 'yansanda ko soji zasu kakkabe duk barayin. Yace barayin sun sansu kuma duk indan suka ji 'yanbanga suna nan to gudu zasu yi. Ba zasu tsaya ba.
Ali Sokoto yayi furucinsa ne lokacin da shi da tawagarsa suka je majalisar dokokin jihar Neja domin su karramata domin gudunmawar da suka ce majalisar na basu. Kakakin majalisar dokokin ta Neja Adamu Usman yace 'yanbangan suna da anfani matuka musamman wajen taimakawa taron kasa. Yace a jihar Borno 'yanbangan ne suka fi bada karfi wurin karfafa tsaro. Shi ma shugaban marasa rinjaye na majalisar Nurudeen Umar yayi karin haske a kan tasirin 'yanbangan. Yace 'yanbanga sun fi kowa wurin tsaro domin a inda aka haifesu suke kuma sun san kowa a yankunansu sabili da haka batagari baya bace masu.
Majalisar dokokin jihar Neja kwanakin baya ta yi doka da ta sa gwamnatin jihar na baiwa 'yanbangan jihar alawus alawus kowane wata lamarin da masu sharhi suka ce yayi tasiri matuka a jihar wajen kawar da batagari.
Ga rahoto

Your browser doesn’t support HTML5