Yanayin Tsaro a Wasu Jihohin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya

Ga dukkan alamu matsalar rashin tsaro ce ta fi daukar hankalin jama’a a wasu jihohin arewa maso tsakiyar Najeriya a daidai lokacin da mahukunta suka dukufa wajen yaki da cutar COVID-19 a kusan duk kasashen duniya.

Jihohin Neja, da Kogi da kuma wani yanki na kananan hukumomin Pategi da Kaiama a jihar Kwara suna ci gaba da fuskantar miyagun ‘yan bindiga masu satar mutane da yin kisan gilla ga jama’a da kuma satar dabbobi, al’amarin da ya jefa dubban mazauna yankunan cikin wani yanayi na tashin hankali da tsoro.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Myetti Allah, Alhaji wakili Damina ya ce ko a kwanan nan maharan sun afka wa wasu Fulani makiyaya a yankin karamar hukumar Dekina a jihar Kogi inda suka hallaka mutum 4 da kuma kashe shanu akalla 9.

Wannan al’amari ya sa rundunar ‘yan sandan jihar kogi daukar matakin shawo kan matsalar. Kakakin ‘yan sandan jihar Kogi, ASP William Aya ya ce sun kama mutum daya da ake kyautatta zaton yana da hannu a harin kuma suna gudanar da binciken gano sauran maharan.

A jihar Neja kuma, bayan rasa daruruwan rayukan mutane a sakamakon hare-haren ‘yan bindigar musammna a yankunan kananan hukumomin Shiroro da Rafi da kuma Mariga, yanzu haka dubban jama’a ne za su gudanar da bukukuwan karamar sallah a wasu wurare da ba gidajensu ba saboda tashin hankalin ‘yan bindiga.

Alhaji Isma’ila Modibbo, shugaban karamar hukumar Rafi, inda lamarin ya fi ta’azzara, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kawo musu dauki ganin yadda mutane da yawa suka yi gudun hijira in ba haka ba za su kara shiga mawuyacin hali.

Ya kuma ce matsalar mahara a karamar hukumar Rafi ita ta fi damun su fiye da annobar cutar COVID-19.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Yanayin Tsaro a Wasu Jihohin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya