Wasu daga cikin dalilan da ke haddasa lalacewar tarbiyyar kanananan yara kamar yadda masana suka bayyana sun hada da rashin bada tarbiyyar kwarai daga iyaye, da kuma irin yanayin da matashi ya sami kansa musamman wajan cudanya da abokai.
Koda shike kowace al'umma da irin nata al'adu da suka bambanta dana sauran al'umma, da dama suna da wasu hanyoyin aiwatar da abubuwa da dama da suke da kama ko kuma alaka da juna.
Tarihi ya bayyana yadda wasu kabilu ke da alaka da wasu musamman ta hanyar kwatanta wasu kalmomi da ke kama da kuma hanyoyin gudanar da wasu al'amuran yau da kullum.
Abin tambaya a nan shine, wacce kabila ce ke da alaka da taka kuma wadanne abubuwa kuke da su da ke kama da juna? ku ziyarci shafin mu na voahausafacebook ko kuma shafin mu mai adireshi www.dandalinvoa.com domin a bayyana ra'ayi.