Horar da matasa a game da matsalolin sauyin yanayin da ake fama da su tare da dabarun yadda za a shawo kan su musamman ma a nahiyar Afirka na daga cikin manufofin shirin CLIMATE REALITY, wanda a duk shekara, ana zakulo matasa masu ra'ayin kare muhalli, masana da kuma masu ilimin kimiyya a fannin Sauyin Yanayi. A bana dai wani rukunin matasa sun hallara a babban birnin kasar Ghana, Accra. Dan rajin kare muhalli ta Najeriya Umar Saleh Anka, wanda ya kasance daga cikin wadanda suka horar da matasan ya yi bayani a game da taron sannan Muhammad Ja'afaru Dankwabia da ke tare da Center for Climate Change and Food Security a Ghana, ya dora da bayanai a game da ingancin horon da matasan suka samu. Sannan bayanan Farfesa Aboubacar Mamman Manzo na jami'ar Tillabery da ke Jamhuriyar Nijar, kuma ya ta'allaka ne akan wata kungiyar Birtaniya da ke nazari akan itatuwa na iyaye da kakanni da yadda za a sarrafa su a matsayin abincin mutane da na dabobi, magani da kuma hanyoyin samun kudin shiga.
A latsa nan domin sauraron cikaken shirin Yanayi Da Muhalli :
Your browser doesn’t support HTML5