Shirin Yanayi Da Muhalli na wannan karon ya mai da hankali ne kan taron shekara shekara da ake yi kan matsalar sauyin yanayi.
Abuja, Nigeria —
A watan Nuwamban kowace shekara ne ake gudanar da taro kan sauyin yanayi na duniya.
A bana, an maida hankali ne akan tanadin kudi a asusun shawo kan asarorin da kasashe masu tasowa suke ta yi a sakamakon matsalolin sauyin yanayi. Taron na karo na 27, da ake wa lakabin COP 27, an fara shi ne a gandun shakatawa na Sharm el-Sheikh da ke Masar tun daga ranar 6 ga watan Nuwamba, wanda kuma za a kammala ranar 18 ga wata.
A latsa nan domin sauraron cikakken shirin A'isha Mu'azu:
Your browser doesn’t support HTML5