Kamar yadda mu ka yi bayani a makon jiya, a watan Nuwamban kowace shekara ne ake gudanar da taro kan sauyin yanayi na duniya.
A farkon makon nan ne Ministan Muhalli na Najeriya ya gabatar da mukalar shugaban kasar Muhammadu Buhari a wajen taron na
COP27 a Sham el-Sheikh na kasar Masar inda yayi nuni da cewar alhakin bada da diyya ga kasashen da suke fama da matsalolin sauyin yanayi ya rataya a wuyar manyan kasasen da suka ci gaba, kasancewar gudunmawar da suke bayarwa wajen gurbata muhalli ta fi yawa.
A wani bangaren kuma an samu nasarar goyon bayan Majalisar Dokokin Amurka kan wannan batu, kwanaki biyu bayan bayanan matsayar ta Najeriya.
A latsa nan don a saurari cikakken shirin daga A’isha Mu’azu:
Your browser doesn’t support HTML5