Yanayi Da Muhalli - Yadda Za A Amfana Da Kudaden Da Aka Ware Na Magance Sauyin Yanayi

Aisha Mu'azu

Al'amuran da suke haifar da matsalolin sauyin yanayi sanannu ne a wurin masu ruwa da tsaki sai dai babbar matsalar ita ce yadda za a tafi da al'amuran samarwa da fitar da kudaden da ake bukata wanda ke tattare da sarkakiya.

Matsanancin zafin da ake fama da shi a fadin duniya ya ja hankalin masana matuka, shugabanni da ma ‘yan rajin kare muhalli inda suke dada kaimi don ganin anyi duk mai yiwuwa wajen inganta yanayin duniya ko za a samu sauki.

A saurari shirin Yanayi Da Muhalli na Aisha Mu'azu

Your browser doesn’t support HTML5

YDM EP 170 -C CLIMATE GREEN FUNDS 7-21-23.m4a