Yanayi Da Muhalli - Kalubalolin Sauyin Yanayi Ga Mata Da Samar Da Makamashi Mai Tsafta

Aisha Mu'azu

Shirin ya tattauna da Dr. Murtala Abubakar Gada, Shugaban Cibiyar Jinsi da Sauyin Yanayi na Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto a game da mahimmancin kare mata daga amfani da makamashi mara tsafta da kuma fahimtar da su hanyoyin samun makamashin girki mai tsafta.

A wani bangaren kuma, Alh. Lawal Yakubu Gada, babban sakataren Africa Foundation For Environmental and Climate Change yayi tsokaci akan mahimmancin gwamnati ta kudiri anniyar daukan matakan tabbatar da samar da makamashi mai tsafta.

A saurari shirin Aisha Mu'azu na YANAYI DA MUHALLI:

Your browser doesn’t support HTML5

YDM - Kalubalolin Sauyin Yanayi Ga Mata Da Yunkurin Samar Da Makamashi Mai Tsafta III 3.mp3