'Yan Yankin Dake Magana Da Harshen Ingilishi A Kamaru Na Fatan Komawa Gidanjensu

Dubban mutanen da yakin ‘yan a ware ya shafa, wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 2000 a yankin kasar Kamaru dake magana da harshen Ingilishi sun dunguma kan tituna su na yin kira ga gwamnatin kasar akan ta yi da gaske game da batun tattaunawar samar da zaman lafiya da ake shirin yi ranar 30 ga watan Satunba, don su sami damar komawa gidajensu.

Yawancin wadanda rikicin ya shafa kusan su 3,000 da gwamnatin kasar ta ce kwanaki 4 kenan suke taruwa a gaban wasu gine-gine, ko dai an kashe ‘yan uwansu ko kuma an lalata masu dukiya. Wasu kuma da su ka jikkata sanadiyar yakin sun ce basu sami damar samun jinya ko magani ba.

Wata mai sana’ar saida kayan miya, ‘yar shekaru 27 da haihuwa mai suna Petra Bannin, wadda ta tsere daga kauyen Nkar dake arewa maso yammacin yankin, ta ce sana’arta ta lalace bayan da aka kashe maigidanta kuma mayakan ‘yan a-waren sun sha sace ‘yayanta maza guda biyu.

Petra Bannin, ta ce “ana bin ta bashi a Bemenda kuma ba ta san inda zata je ta samo kudi ba. ta kuma ce ta biya mayakan kudin fansa amma har yanzu su na barazanar zasu sake sace ‘yayata. Ga shi ‘yayan ba za su iya zuwa makaranta ba, a cewarta, don haka ta na fatan shugaba Paul Biya zai nemo hanyar da za a warware wannan matsalar.

Esther Njomo, mai kula da harkokin wata kungiyar wanzar da zaman lafiya ta mata a arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar, ta ce su na yin kira ga shugaba Biya akan ya saki shugabannin yankin dake magana da harshen ingilishi da aka tsare a matsayin wata alama dake nuna cewa da gaske yake akan tattaunawar da ake shirin yi gobe.