Mai horar da ‘yan wasan super Eagles na Najeriya Sunday Oliseh, ya jaddada cewa ‘yan wasansa sun taka rawar gani a karawar da suka yi da takwarornsu na Jmahuriyar Dimokradiyar Congo, duk da cewa an doke su da ci 2-0 a wasan sada zumunta da kasashen biyu suka buga.
Dieumerci Mbokani da Jordan Nkololo ne suka ci wa Congo kwallayensu a lokacin da suka lallasa tsoffin zakarun gasar nahiyar Afrika a filin wasa na De’ l’Oie , Vise.
A cewar Oliseh ya yi amfani da ‘yan wasa ne da ke hanu, saboda mafi yawan wadanda ya gayyata basu samu takardun visa ba, kuma ya ce ya yi alfahri da rawar da suka taka
Ya kuma kara da cewa, su suka mallaki wasan duk da cewa an samu cikas a wasu bangarori, yana mai jaddada cewa a lokacin da dan wasa Alexander Iwobi ya shiga filin, ya nuna kwazo kuma sauran ‘yan wasa irinsu Shehu Abdullahi su ma sun taka kwallo a karawar su ta farko.
Burin ‘yan wasan na Super Eagles a cewar Oliseh shi ne, su samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekarar 2017.