'Yan Wasan Super Eagles Ba Za Su Kada Kuri'a Ranar Asabar Ba

  • Ibrahim Garba

Babban jami'in kwallon kafa na Super Eagles na Najeriya, Pascal Patrick da sauran 'yan kulob din

Yanzu dai ta tabbata cewa ‘yan kulob din kwallon kafar Najeriya na Super Eagles, ba za su samu damar kada kuri’a a zaben Najeriya na ranar Asabar ba, saboda za su tafi Afirka Ta Kudu don gudanar da abin da su ka kira wani aiki na kasa a lokacin wannan zaben. To amma ‘yan wasan na Super Eagles sun yi wa kasarsu addu’a da fatan alheri, tare da kiran ‘yan uwansu ‘yan Najeriya da su gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, da gaskiya da kuma adalci.

Sabon jami’in gudanarwar Super Eagles din, Patrick Pascal, y ace ya kamata zaben da ke tafe ya zama wata dama ta samun Shugaban da zai gudanar da komai don daukaka muradun ‘yan Najeriya baki daya. Don haka ya yi kira ga masu kada kuri’a da su kai zuciya nesa cikin kowane irin hali.

Najeriya za ta gwabza da Afirka ta Kudu a wata gasar zumunci ta kasa da kasa, wadda za a yi a Nelspruit ranar Lahadi.

Your browser doesn’t support HTML5

'YAN SUPER EAGLES da ZABE