Abin da aka dade ana tsammani, 'Yan wasan Najeriya sun yi nasarar lashe lambobin yabo a gasar Wasanni ta Nahiyar Afirka da aka gudanawar a kasar Marocco, inda Najeriya ta kai zuwa mataki na biyu a kan teburin lambobin yabo.
A karshen wasannin da akayi a jiya Alhamis, Kungiyoyin wasanni na Nigeriya sun tara lambobin yabo guda 103, wadanda suka hada da zinare 40, azurfa 28 da tagulla 35.
A wasan karshe na kwallon badminton, na mata, Dorcas Adesokan ta samu kyautar azurfa, ta doke Johanita Scholtz ta kasar Afirka ta kudu da ci biyu da babu ko daya 2-0, yayin da a na maza kuma, Anuoluwapo Opeyori ya ci lambar zinare, inda ya doke abokin karawarsa Julien Paul, na kasar Mauritius da ci biyu da babu ko daya 2-0, a wasan karshe.
A wasan dambe, Temitope Shogbamu ta doke Alcinda Panguane ta kasar Mozambique da ci 4-1 a wasan karshe na mata, wanda ya baiwa Najeriya lambar yabo ta farko a wasan dambe. Ayoola Osoba ya yi rashin nasara a hannun abokin karawarsa na kasar Mauritius, Merven Clair, wanda ya ci lambar zinare a wasan karshe na maza.
A gasar tseren kwale-kwale wanda sabon wasa ne ga ‘yan Najeriya, Ayomide Bello ta lashe wasan karshe na mita 500m, a cikin awa biyu da minti talatin da bakwai 2: 37.13.