‘Yan Wasan Ghana Black Stars Zasu Samu $5000 Kachal

'Yan Wasan Ghana

Da alamar za’a rage kudaden da za’a biyar ‘yan wasan kwallon kafa na Ghana Black Stars, na shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Idan kudin da hukumar wasani ta kasar Ghana tace zata baiwa ‘yan wasan ya tabbata, ko shakka babu ‘yan wasan na Ghana Black Star dai zasu ga ragowar sama da rabin kudin da aka saba basu.

Hukumar matasa da wasani ta kasar Ghana tace za’a ba ‘yan wasan dalar Amuka, dubu biyar ne kachal, don shiga gasar cin kofin Afirka, da za’a yi a kasar Equatorial Guinea.

A wani labarin kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick, ya musanta rahotanin dake cewa hukumar san a fuskatar masin lamba daga fadar Gwamnatin Najeriya, domin sake baiwa Koch din Najeriya, Stephen Keshi, kwantaregi domin horas da ‘yan wasan Super Eagles, kafin karshen wannan shekaran, koda yake dai Stephen Keshi, ya gaza kai Najeriya, zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2015.

Your browser doesn’t support HTML5

Gasar kofin Nahiyar Afirka - 1'00"