‘Yan tawayen Syria da ake kira Syrian Democratic Forces ko SDF a takaice, da Amurka take marawa baya, sun ce a yau Talata sun kwace ragowar sassan birnin Raqqa dake karkashin ikon mayakan sakai na ISIS.
Mai magana da yawun SDF, wacce ta kunshi mayakan sakai na Kurdawa da kuma Larabawa, ya fadawa manema labarai cewa yakin da suke yi a Raqqa ya kare. Kungiyar dake sa ido kan hakkokin bil adama ta Siriya wadda ke da gindin-zama a Birtaniya, itama ta bada sanarwar an ‘yanta Raqqa.
Dakarun SDF sun afkawa babban dandalin wasanni wanda shine cibiya ta karshe da ta rage hanun ‘yan bindigar ISIS a birnin bayan kwato Asibiti wanda suke amfani da shi a matsayin cibiyar kula da fadace fadacen da mayakan sakan suke yi.
Tun a cikin watan Yunin bana ne dai aka fara yunkurin murkushe tsagerun daga Raqqa, wanda ya sami taimako da jiragen sama na yaki, da wasu agaji da rundunar taron dangi karkashin Amurka ta samar.