'Yan tawayen Sham Sun Dauki Alhakin Harin Bam

Ministan tsaro, da mukaddashin ministan tsaro da wani janar na sojan gwamnatin Sham sun mutu a tashin bam a birnin Damascus

‘Yan tawayen kasar Sham sun dauki alhakin wani bam da ya tashi jiya laraba ya kashe ministan tsaron kasar tare da wasu manya biyu a lokacin wani taron manyan jami’ai a birnin Damascus.

‘Yan tawayen sun yi barazanr kai karin hare-hare. Suka ce harin bam na jiya laraba shi ne mafarin kawo karshen gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Bam din ya kashe ministan tsaro Daoud Rajha, da mukaddashin ministan tsaro kuma surukin shugaba Assad, Assef Shawkat. Akwai kuma wani janar na sojan Sham da shi ma ya rasa rai a tashin bam din.

Wasu rahotanni suka ce wani dogari ne a wurin ya kai harin, yayin da wasu kuma suka ce an boye bam din ne a cikin wata ‘yar jaka.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya tattauna batun kasar Sham ta wayar tarho da shugaba Vladimir Putin na Rasha. Sun lura da bambancin dake tsakaninsu kan batun na Sham, amma kuma sun bayyana gurinsu na ganin an kawo karshen wannan tashin hankali.

Dakarun Sham da ‘yan tawaye sun sake gwabzawa jiya laraba a birnin na Damascus. An ce mutane kimanin 100 ne suka mutu a fadin kasar.