An kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan tawayen Mali da ke takaddama da juna a yankin Kidal da ke arewacin Mali.
Wannan yarjejeniya da aka bai wa suna "Ayyanawar Niamey" ta biyo bayan tattaunawar da aka yi na tsawon kwanaki a tsakanin kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta "Coordination de Mouvement de l'Azawad" ko CMA a takaice, da kuma wata kungiyar mai goyon bayan gwamnati da ake kira "Plateform de 14 Juin" da nufin kawo karshen fada a wannan yanki na Kidal.
Cimma yarjejeniyar, ta kuma biyo bayan kokarin firayim ministan Nijar, Brigi Rafini, na shiga tsakanin wadannan sassan domin tabbatar da sulhu, a tattaunawar da ta gudana a birnin Yamai.
Wani dan tawayen yankin na arewacin Mali, Ahmed Ouagayya, yace yarjejeniyar ta tanadi kafa hukumomin rikon kwarya, wadanda zasu yi kokarin sanar da jama'ar wannan yanki abinda yarjejeniyar ta kunsa.
sai dai kuma wani tsohon kakakin wata kungiyar 'yan tawaye a arewacin nijar, Kausal Maiga, ya bayyana tababar dorewar wannan yarjejeniya, yana mai cewa kungiyoyin nan sun sha cimma yarjejeniya su na karyawa.
Domin jin karin bayani saurari cikakken rohotan Suleiman Mumini Barma daga Yamai.
Your browser doesn’t support HTML5