Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan tawayen kasar Syria sun cimma yarjejeniyar ajiye makaman su a kudu maso yammacin wuraren dake kusa da yankin Golan, wanda Isra’ila ta mamaye.
WASHINGTON D.C —
Wannan yarjejeniyar ta bukaci dakarun gwamnatin Syria, su koma wuraren da suka rike a lardin al-Quneitra kafin barkewar boren da aka yiwa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad a shekarar 2011. Duk ‘yan tawayen da ba su amince da ka’idojin yarjejeniyar ba, za a barsu su je wasu yankunan da ‘yan adawa suke rike da su a Syria.
Dakarun Syria, dake samun goyon bayan dakarun Rasha, sun kaddamar da wasu hare-hare don kwato wurare na karshe a kudu maso yammacin kasar dake hannun ‘yan tawayen, wurin da mutane kimanin 160,000 suka makale.
A halin da ake ciki kuma, a yau Alhamis aka kammala kwashe akalla mutane 7,000 mazauna garuruwan Foua, da Kfarya dake goyon bayan shugaba Assad a arewacin Syria.