Wata bataliyar mayakan sa kai a kasar libya ta mamaye ofishin jakadancin kasar Nijer a birnin Tripoli ta tayar da hankalin ma’aikatan ofishin. Ko da yake babu asarar rayuka, amma mayakan sa kan sun jefa ma’aikatan ofishin jakadancin na kasar Nijer cikin rudu da fargaba wanda hakan ya sa ma’aikatar harakokin wajen kasar jamahuriyar Nijer ta kira wani taron manema labarai a birnin Niamey takamaimai don bayyanawa ‘yan kasa abun da ya faru.
Sakataren Ma’aikatar harakokin wajen kasar Jamahuriyar Nijer Mallam Abbani Ibrahim Sani ya shaidawa ‘yan jarida abun da ya faru a ofishin jakadancin na kasar Nijer a kasar ta Libiya.
Your browser doesn’t support HTML5
Rahotanni sun ce mayakan sa kan na kasar Libiya sun yi hakan ne kawai domin su mayar da martani game da tsaurara matakan tsaron da gwamnatin kasar Nijer ta dauka a ofishin jakadancin kasar Libiya da ke Niamey, babban birnin kasar jamahuriyar Nijer.
Wakilin Sashen Hausa a Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ne ya aiko da rahoton.