‘Yan takarar shugabancin kasar Faransa Marine Le Pen da Emmanuel Macron sun tafka muhawara mai zafi wadda aka nuna a gidan talabijin jiya Laraba, ‘yan kwanaki kafin a yi zaben gama gari a kasar.
WASHINGTON, DC —
Mrs. Le Pen ta bayyana abokin adawarta a matsayin rikakken dan jari hujja wanda ke da rauni wajen yaki da ta’addanci, shi kuma ya kira Marine din a matsayin makaryaciya mai tsattsauran ra’ayi.
A jawabin ta na farko lokacin muhawarar, Le Pen ta kira tsohon ministan harkokin tattalin arzikin a matsayin “dan takara mai ra’ayin “kowa yayi abinda yake so”.
Rashin ayyuka a kasar na cikin abubuwan da ‘yan takarar suka tattauna. Macron ya yi kira akan a saukaka ka’idojin gwamnati da na kanana da kuma matsakaitan sana’o’i, ita kuma Le Pen ta yi alkawarin zata kara haraji akan kayayyakin kamfanonin kasashen ketare.