Shekarar zabe a Najeriya na cike da bayanan alkawulan da ‘yan siyasa kan yi na in an zabe su zasu aiwatar. Abin da ma ya fi bada ta’ajjabi shine hatta ‘yan takarar gwamnatin tarayya ko wanda jiha ta tsayar, zaka ji suna cewa zasu kawo sauyi daga wadanda suke sa ran gada. Amma kalilan ne ke cewa zasu dora daga inda na jiya suka tsaya.
Shekara kusan goma sha shida ke nan da demokradiyya a Najeriya amma alkawulan da ‘yan siyasa ke yi basu wuce shimfda titituna, samar da ruwan sha ko magani a asibiti. Abin da za a ce ya karu shine alkawulan dakatar da zubar da jini da hasarar dukiya ba bisa hakkin shari’a ba.
A wani zauren ganawa na ‘yan takara da Katsinawa suka shirya a birnin tarayya Abuja, wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu EL-Hikaya ya halarci taron, ya kuma gaya ma muryar Amurka cewa yaji mai neman takarar Gwaman a jihar Katsina Sanata Ibrahim Ida, ya dauko wani sabon salon Kamfe. Harma wani mai tambaya ya mike tsaye yace "me ya sa ‘yan siyasa ke daukar alkawali amma da zarar sun hau kan kujera sai su manta"? Shi kuma Sanata Ida tabbatar da cewa tambayar na da ma’ana.
Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5