A karo na biyu wasu ‘yan ta’adda, sun kai wani hari a kasar Jamhuriyar, Nijar, inda suka yi batakashe.
WASHINGTON, DC —
A karo na biyu wasu ‘yan ta’adda, sun kai wani hari a kasar Jamhuriyar, Nijar, inda suka yi batakashe, da jami’an tsaron kasar ta Jamhuriyar, Nijar, wanda yayi sanadiyar, mutuwar, wani Jami’in tsaro daya.
Wannan arangamar da akayi tsakanin sojoji da ;yan ta’adda, ya faru ne awani gari, bani Bangu, mai tazaran sama da kilomita 240 daga babban birnin Niamey.
‘Yan ta’addan sun samu nasarar kwace mota daya daga hannun sojojin inda kuma suka kona wata motar domin kara gurgunta sojojin.
Kakakin rundunar sojojin jamhuriyar Nijar Kanal, Mustapha Laudiri, ya tabbatar wa wakilin Murya Amurka Abdoulaye Mamane Amadou, afkuwar lamarin, inda yace hukuimar Soji, na ci gaba da binciken harin da ‘yan ta’addan suka kai.
Your browser doesn’t support HTML5