Ganin tabbatar cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana ya sa gwamnatin jihar Neja ta shiga fadakar da matasa har ma da iyayensu.
Alhaji Danladi Ndayabo kwamishanan yada labarai na jihar yace suna kiran iyayen yara kada su bari wasu 'yan tsagera su janye hankulan 'ya'yansu shiga yin abun da bai dace ba kamar shiga rikici. Yace su a PDP babu ruwansu da rikici dalili ke nan koina suka je aka tsokanesu sai su barsu. Nufinsu ne a yi zabukan cikin lumana.
Su ma 'yan siyasan dake son a zabesu batun zaman lafiya ya shigesu. Alhaji Umar Nasko dake neman kujerar jihar Neja a karkashin PDP ya roki matasa wadanda ya kira 'yanuwansa da su yiwa Allah su natsu domin idan babu natsuwa to za'a shiga matsala.
Shi ma dan takarar gwamna a karkashin APC Alhaji Abu Sani Bello yace suna daukan mataki a bangarensu. Sun yi taro da kwamishanan 'yansandan jihar kuma ya gargadesu a yi zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da rigima ba. Yace su ma suna gaya wa magoya bayansu matasa cewa a yi zaben cikin kwanciyar hankali
Gwamnan jihar Babangida Muazu Aliyu yace a zamaninsa Allah ya basu zaman lafiya sabili da sun samu nasarar danne banbance banbancen addini da na kabilanci.
Masana sun ce bin doka da yin adalci a lokacin zaben zasu taimaka wajen wanzar da zaman lafiya.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5