‘Yan siyasar kasar Kamaru Sun Kalubalanci Shugaba Paul Biya.

  • Ladan Ayawa

Shugaban Kamaru, Paul Biya

‘Yan siyasa kasar Kamaru sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna kyamar su ga tsayawa takarar shugaban Paul Biya

Wakilin Murya Amurka dake kasar Moki Edwin Kindzeka ya aiko da rahoto da Halima ta fassara kuma ta gabatar kamar haka.

A kasar Kamaru 'yan adawa sun kalubalanci 'yan sanda suka ci gaba da zanga-zangar nuna kin amincewa da yunkurin jam'iya mai mulki na neman shirya zabe tun lokacin bai yi ba. 'Yan adawar suka ce shugaban kasar Kamaru Paul Biya mai shekaru 84 a duniya ya na neman yin mulkin mutu-ka-raba bayan ya riga yayi shekaru 34 ya na mulkin kasar. Daga lokacin da suka kaddamar da zanga-zangar a ranar talatar da ta gabata ya zuwa yanzu an raunata da dama daga cikin su, kuma an kama wasu. An bukaci masu zanga-zangar sun sanya bakaken kaya ranar Lahadi. Ga fassarar rahoton da wakilin Muryar Amurka Moki Edwin Kindzeka ya aiko daga birnin Yaounde, Halima Djimrao ta fassara kuma ta gabatar tare da taimakon Ladan Ibrahim Ayawa:

Halima ce ta fassara rahoton kuma ta gabatar 2’56

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan siyasar kasar Kamaru Sun Kalubalanci Shugaba Paul Biya. 2'56