Babban jimiin kula da kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, yace ‘yan siyasa irin su Geert Wilder na kasar Jamus da dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin tutar jamiyyar Republican Donald Trump suna anfani da shuka tsoro da alkawarin abin da bai taba samuwa ba domin naman kuriaar mutane.
WASHINGTON DC —
Babban jamiin yana magana a jiya littini a taron tsaro da sharaa wanda akayi a Hague.
Zeid Ra’ad Al-Hussein yace ‘yan siyasan suna dogaro da bayanan karya da kuma wuce makadi da rawa.
Zeid yace dabarar yin hakan shine su sa mutane rawar jiki, tare da shuka tsoro cikin zukatan su kana daga bisani sai suce musu gamafita akan duk wasu matsalolin da suka zayyana
Zeid dai ya danganta kalaman nasa ne musammam ga Wilder wanda a cikin watan Agusta yasa a cikin manufofin kanfe dinsa cewa yana kira ga Jamus data hana bakin haure musulmai shigowa cikin kasar, tare da rufe masallatai da makarantun musulmai, sai dai Wilder yayi wa Zeid lakabi da kalamin zagi mara dadi shi da MDD din.