'Yan Sintiri A Adamawa Sun Kama 'Masu Satar Mutane

Jami'an Bada Kariya Ga Fararen Hula Na Civil Defense

Jami’an tsaron farin kaya na "sibil difens" a jihar Adamawa sun samu nasarar murkushe masu satar mutane domin neman kudin fansa. Wannan nasarar ta na zuwa ne a lokacin da jama’a ke kasa barci sakamakon ayyukan masu garkuwa da jama’ar.

Baya ga masu garkuwa da jama’a rundunar tsaron farin kayan ta 'sibil difens', ta kuma samu nasarar cafke barayin shanu da wasu masu safarar miyagun kwayoyi.

Da yake yi wa manema labarai karin haske a kan wannan nasarar da aka samu, kwamandan rundunar tsaron farin kayan ta 'sibil difens' a jihar Adamawa Alhaji Nuruddin Abdullahi ya ce, sun samu nasarar ce tare da hadin gwiwar sojoji inda ya kuma ce za su ci gaba da baza komarsu don cafko irin wadannan bata gari dake hana jama’a barci a yanzu.

Bincike ya nuna cewa, yanzu haka matsalar ‘yan fashi da makami da kuma garkuwa da jama’a na neman shafar ayyukan noma, musamman a jihohin arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya kai hadakar kungiyoyin bunkasa harkar noma da cimaka ta NECAS, yunkurowa wajen hada karfi da karfe da jami’an tsaro don tabbatar da tsaro ga manoma, Alhaji Abubakar Sadik Umar Daware, shi ne shugaban NECAS da ke zama shugaban cibiyar a jihohin arewa maso gabas, ya ce akwai matakan da suka dauka a yanzu.

Ga dai rahoton wakilinmu a jihar Adamawa Ibrahim Abdulaziz:

Your browser doesn’t support HTML5

AN YI NASARAR MURKUSHE MASU GARKUWA