Dubban ‘yan Shi’ar sun hadu ne daga sassa daban-daban na sassan Najeriya da Jamhuriyar Nijar, inda suka rankaya cikin birnin N’konni da ke jihar Tahoua dake Nijar. Inda suka taru don yin bikin Maulidin Annabi Muhammad Tsira da Aminci su tabbata a gareshi.
Sun yi Amfani da wannan dama wajen nuna takaicinsu na ‘yan uwan da aka kashe musu a birnin Zazzau da ke jihar Kaduna a Najeriya da suka ce daruruwa aka bindige musu bisa zargin sun tarewa shugaban sojoji Tukur Buratai hanyar wucewa.
Shugaban ‘yan shi’a na birnin na N’konni Malam Usman Bin Isa, ya bayyana cewa suna taya murnar ranar haihuwar Annabin tsira ne. sannan su nunawa duniya cewa sub a masu son tashin hankali ne, kuma bas u ji dadin yadda aka yiwa ‘yan uwansu a Zaria ba.
Sun kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da cewa ta sakar musu shugabansu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky da ake tsare da shit un bayan arangamar tasu da Sojin Najeriya. Daga karshe sun cewa wakilinmu Harouna Mamane Bako cewa, suna nunawa duniya irin zalincin da aka yi musu ne. ga muryar rahoton da ya aiko mana.
Your browser doesn’t support HTML5