'Yan Shi'a Sun Kama Wani Birni a Yemen

Dakarun Yemen suna shirin kai hari

'Yan Shi'a da suka dade suna yiwa gwamnatin kasar Yemen tawaye sun kama wani birnin kasar lamarin da yasa dubban mutane sun fice daga birnin.

:

A Yemen ‘yan shi’a da suke tawaye sun kama wani birnin Amran jiya dake arewacin babban binrin kasar, al’amarin da ya tilastawa dubban mutane tserewa domin kare lafiyarsu.

A jiya talata ce ‘yan tawayen kungiyar da ake kira Hawthi suka kama birnin bayan sun shafe watanni suna gwabza fada da wasu kabilu da suke samun goyon bayan sojojin kasar

Shaidun gani da ido sun bada labarin ganin gawarwaki suna zube ko ta ina a gefen tituna. Kungiyar agajin kasar ta Red Crescents tace kimanin iyalai dubu 10 ne suka gudu daga binrinn domin kaucewa fadan da ake yi.

Gwamnatin kasar bata ce uffan ba. Amma jakadan MDD na musamman kan rikicin na Yemen yayi kira ga duka sassan biyu su daina fada kuma su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da ya shiga tsakani aka cimma cikin watan jiya.

‘Yan tawayen kungiyar Hawthi sun dade suna gwabza fada kan zargin gwanatin kasar tayi watsi dasu na shekaru masu yawan gaske.