A Najeriya wasu matasa 'yan daba da aka fi saninsu da sunan 'yan "Sara- Suka" a jihar Bauchi, kimanin su 500 ne suka yi shelar sun tuba daga ayyukan ta’addanci, suka kuma mika makamansu ga jami’an 'yan sanda.
Matasa ‘Yan sara-sukan sun ce sun ajiye makaman fadansu ne, biyo bayan nazarin da su ka yi don son zama tare da sauran al’umma lami lafiya, sannan sun bukaci gwamnati ta samar masu da abin da zai taimake su don su inganta sabuwar rayuwar da za su shiga.
Wasu daga cikin tubabbun matasa 'yan Sara-sukan sun yi bayanin ayyukan ta’addancin da suka aiwatar gabanin tuban na su a yanzu.
A jawabin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Habu Sani Ahmadu, ya shaida cewar wannan babban ci gaba ne a yaki da matsalar tsaro da ake yi a fadin jihar.
A jawabin da ya gabatar shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Bauchi, Alhaji Abubakar Kari, a madadin gwamnan jihar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi, ya ce gwamantin jihar ta tsara shirye- shirye don taimakawa matasan.
Your browser doesn’t support HTML5