Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya tabbatar da cewa zai binciki sabon tashin hankalin da ya bullo a Jihar Zamfara.
Zuwa yanzu dai ana jiran sabbin bayanai kan alkawarin binciken, dalilan dawowar fitina a wasu sassan Zamfara tare da harin 'yan ta'adda a Jihar Adamawa.
Sufeto janar din ya bayyana haka ne yayinda yake amsa tambaya kan fitinar da ta auku a Karaye da ke yankin karamar hukumar Gumi a jihar Zamfara, inda mahara su ka hallaka akalla mutum 20.
Sabon farmakin ya sanya al’ummar dake zaune a kauyen yin hijira, inda su ke kira ga gwamnatin tarayya ta dauki sababbin matakan dakile kalubalen.
An samu tankiya tsakanin gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun da tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari, kan wannan damuwa da masu sharhi ke ganin matakin kare jama’a ya kamata a dauka maimakon muhawarar siyasa ta jam’iyyun PDP da APC.
Saurari cikakken Rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5