Shugaban kungiyar Network For Justice, Aminu Sule ya ce kowa ya sani 'yan sanda suna goyon bayan gwamnati
WASHINGTON, DC —
Shisshigi da katsalandan din da ‘yan sandan Najeriya ke ci gaba da yi a cikin al’amuran siyasar kasar sun sa majalisar wakilai ta kira babban Sufeton ‘yan sandan kasar Mohammed Dahiru Abubakar ya je yayi ma ta bayanin abun da ke faruwa, yayi karin haske musamman ma game da al’amarin baya-bayan nan da ya faru lokacin da wasu ‘yan sanda dauke da bindigogi suka mamaye gidan gwamnatin jahar Kano na Abuja a karkashin jagorancin wani DPO, da kuma dirar mikiyar da ‘yan sandan Najeriya suka rika yi bi da bi a jere su na tarwatsa tarurrukan magoya bayan sabuwar PDP da ma tarurrukan gwamnoni bakwai da suka bijirewa jam’iyar PDP mai mulkin Najeriya. Game da duka wadannan abubuwa ne Ibrahim Ka’almasih Garba ya tuntubi Malam Aminu Sule babban shugaban kungiya mai zaman kan ta, ta Network For Justice, mai kare hakkokin ‘yan Adam.
Your browser doesn’t support HTML5