'Yan Sandan Najeriya Sun Cafke Mutane 4 Da Harsasai 441 A Zamfara

Iyali Da Safarar Harsasai

Jami'an 'Yan sanda sun yi nasarar cafke wani magidanci da mai dakinsa dauke da 'yar karamar yarinya a yayin da suke kokarin kai wa 'yan bindiga harsasasai cikin daji.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen karamar hukumar Anka ta samu nasarar cafke wasu ma’aurata da ake zargin ‘yan bindiga ne ko kuma suna da alaka da 'yan bindigar da kuma wasu mutane biyu dauke da harsasai 441 da aka yi niyyar kai wa ‘yan bindiga a yankin.

Wadanda ake zargin su ne Mamuda Makakari da matarsa Kuluwa Mamuda Wanda ke goye da karamar yarinya tare da wasu 'yan mata biyu, Maryam Sani da Amina Jijji, a sa'adda suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin ‘yan bindiga a dajin Makakari.

Rahotannin sun bayyana cewa wadanda ake zargin su na hanyar su ta kai wa wani dan bindiga da ke cikin dajin na Mamakari harsasan bindiga ne lokacin da aka kama su.

Karamar Hukumar Anka dai ta kasance wani wuri da ‘yan fashi ke yawan kai hare-hare akai akai, sannan yankin ya yi kaurin sunan tara yawan dabobin 'yan bindiga ciki har da dabar wadanda ke da alaka da Kachalla Halilu Sububu kasurgumin dan bindigar da aka kashe a Kwanan nan.

Hakazalika, akwai wuraren hakar ma'adanai mallakin 'yan bindigar a yankin.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa daga Gusau aka aike da lambar wayar dan aiken da kuma ta wanda zai amshi sakon, lamarin da ya nuna cewa suna shiga tsakani a harkar cinikin makamai.

Yanzu haka dai hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike amma ba su kai ga fitar da wani bayani ba a hukumance ba.