Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta kama wasu barayi matasa masu satar mutane da suka sace wani dattijo dan shekara 80 da haihuwa, suka karbi naira miliyan 8 kudin fansa kafin suka sako shi.
Haka kuma yan sandan na jihar Oyo sun kuma kama wasu barayin motocin alfarma, harma sun samu bindigogi da dama daga hannun barayin.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Oyo Alhaji Musa Mohammed Katsina ya shedawa wakilin sashen Hausa, Hassan Umaru Tambuwal cewa mutane hudun da aka kama Fulani ne daga jihar Kwara. Yace sune suke tadawa mutane hankali suna sace su.
Alhaji Musa yace a lokacin azumi suka je wani kauye a jihar Kwara suka sace wani dattijo. Sai da aka basu naira miliyan takwas kafin suka sako dattijon
Da suka ji dadin kudin ne, sai suka shiga jihar Oyo a wani yunkurin sace wani Sarki. A lungun da suke kitsa wannan makarkashiya Allah yasa yan sandan boye suka samu labari. Suka je suka kama na farko.
Da taimakon Allah kuma auka je har jihar Ekiti suka kama mutane biyu a can. An samu shanu 12 da manyan motoci guda 3 na alfarma. Kwamishinan yan sanda yace dukkan wadanda aka kama matasa ne ko kuma yara, domin baban cikin su shine mai shekara 21.
Haka kuma yan sanda sun samu wata babar mota dankare da mai durin 75 da barayin suka sato.
Your browser doesn’t support HTML5