‘Yan Sandan Girka Sun Gwabza Da Ma'aikatan Da ke Zanga-zanga

  • Ibrahim Garba

Bodies of Morsi supporters killed early Saturday in clashes with security forces are seen in a makeshift morgue in Cairo, July 27, 2013, (Elizabeth Arrott/VOA).

‘Yan sandan kwantar da tarzomar Girka sun fafata da masu zanga-zanga yau a Laraba, a yayin da dubban mutane ke zanga-zanga kan matakan tsimin da gwamnati ta dauka don tsamo kasar daga matsalar dinbin basussukan da ta fada ciki.

Sama da ma’aikata 30,000 da ke yajin aiki ne su ka yi gangami zuwa Majalisar Kasar ta Girka da ke Athens, babban birnin kasar, inda ‘yan sanda su ka yi ta harba barkonon tsohuwa da bama baman baza hayaki kan masu zanga-zangar das u kuma k eta jifa da duwatsu.

A kalla mutum guda ya sami rauni.

Gangamin wani sashi ne nuna rashin jin dadi da bangaren kwadago ke yi a wannan shekarar. Manyan kungiyoyin a Girka da ke wakiltar ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu na zanga-zanga ne game da matakan rage kashe kudin da Firayim Minista George Papandreaou ya dauka.