"Taron 'Yanci" wanda ya kunshi galibin masu tuka manyan motocin daukar kaya, ya fara ne a matsayin wani yunkuri na adawa da bukatar allurar riga-kafin Canada ga direbobin kan iyaka. Amma tun daga wannan lokacin ya zama wani yunkuri na yin adawa da tsauraran matakan Firayim Minista Justin Trudeau na yakar cutar.
A cikin garin Ottawa, gida ga majalisar dokokin Canada, babban bankin kasa, da gine-ginen da suka hada da ofishin Trudeau, sun kasance a kulle bayan da manyan motocin dakon kaya suka mamaye tituna. Har cikin dare ana jin su suna dana hon da kuma wasan wuta akai akai, lamarin da ya kawo cikas ga zaman lumana na mazauna birnin.
A yau litinin ne za a yi zaman sauraren karar da aka shigar na neman a ba da umarnin dakatar da zanga zangar masu tuka manyan motocin.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump da shugaban kamfanin Tesla (TSLA.O) Elon Musk sun yabawa masu tuka manyan motocin.
Gwamnatin Canada ta ki yin watsi da wannan batu. Trudeau, wanda ya kebe kansa bayan gwajin kamuwarsa da COVID-19, ya ki bada umarnin amfani da sojoji don wargaza zanga-zangar.
Trudeau da iyalinsa sun bar gidansu na cikin gari bayan da masu daukar kaya suka iso garin Ottawa kuma ba a bayyana inda yake ba saboda matsalolin tsaro.
A karshen mako, zanga-zangar ta mamaye wasu manyan biranen Canada, gami da babban birnin hada-hadar kudi na Toronto. Zanga-zangar dai ta kasance cikin lumana.
Yawancin al’umma Canada suna bin matakan kiwon lafiya na gwamnati kuma kusan kashi 79% na mutanen sun ɗauki kashi biyu na rigakafin. Amma kuri'un da aka yi a baya-bayan nan sun nuna takaici game da matakan allurar rigakafi da ake cigaba da karawa.
- REUTERS