Rundunar yan sandan Jihar Neja a Nigeria tace ta samu nasarar kwato wani alkalin da yan bindiga suka yi garkuwa da shi a makon da ya gabata. Da yammacin jiya Alhamis ne rundunar yan sandan ta bada sanarwar kubutar da alkalin da yake aiki a wata kotu a karamar hukumar Rafi.
WASHINGTON DC —
Wasu rahotanni sun nuna cewar sai da aka biya wasu makudan kudade kafin samun nasarar karbo wannan alkalin mai suna Ahmed Abubakar Kontagora. Sai dai kakakin yan sandan jihar Neja ASP Dainna Abubakar ya musunta wannan rahotannin inda yace babu wasu kudade da aka bayar kafin karbo alkalin.
Kakakin yan sandan yace suna nan suna ci gaba da bin kadin wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin tabbatar da an hukunta su.
Kanal M. K. Maikundi mai ritaya, wanda shine mai ba gwamnan jihar Neja shawara a kan sha’anin tsaro, yace gwamnati ta damu matuka a kan matsalar satar mutane don neman kudin fansa. Kanal Maikundi yace gwamnati na nan tana daukar matakai don kawo karshen wannan lamari.
Your browser doesn’t support HTML5