‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 30 Da ake Zargi Da Satar Muatane A Jihar Nasarawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama mutane guda Talatin da take zargi da satar mutane, fashi da makami da kuma wasu manyan laifuka a yankin karamar hukumar Nasarawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, Abubakar Sadiq Bello, ya ce sun kama mutanen ne a wani samame da suka kai biyo bayan yawan aikata laifuka a sassa daban daban na jihar.

Ya ce “lallai mun kama mutane kusan Talatin da muke zargi da aikta laifuka irinsu satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makami da sauransu, kuma mun gudanar da wannan samame ne tare da hadin gwiwar Fulani da ‘yan banga, kuma mun kama su ne can tsakanin Nasarawa, zuwa maraba wajan tsaunukan da ke yankin”

Da ya ke amsa tambayar wakiliyar sashen Hausa na muryar Amurka, Zainab Babaji, akan matakan da suka dauka na kare rayukan jama’a, kwamishinan ya bayyana cewa sun yanke hukuncin kai samame kan tsaunikan dake yakunan ne domin sun sami rahoton cewa can ne matattarar wadannan miyagun mutane.

Daga karshe ya yi kira ga daukacin jama’ar jihar da su sani cewa aikin tsaro ba na jami;an tsaro kadai bane, ya bukaci jama’a su hada hannu da taimaka masu da shawarwari ko kuma su bada rahoto akan duk wasu mutane masu nasaba da aikata muggan laifuka da ke sajewa da jama’a.

Attahiru Ahmed, ya bayyana cewa jama’r yankin na matukar fama da barayi kamar yadda kwanakin da suka gabata aka sace diyarsa sa’annan kuma aka bukaci ya biya kudin fansa.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji domin Karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 30 Da ake Zargi Da Satar Muatane A Jihar Nasarawa