Jami’an tsaron da su ka mamaye Majalisar Dokokin Jihar Naija bayan da aka caccanza shugabannin Majalisar, a yanzu sun janye. Hasalima, Majalisar ta yi zama a jiya Laraba karkashin jagorancin sabon Kakakin Majalisar Honorabul Isah kawu.
Wakilinmu a jihar ta Naija Mustapha Nasiru Batsari ya tuntubi Mataimakin Kakakin Majalisar Honorabul Bello Agwara tun jin ra’ayinsa kan kawo karshen mamayar da aka yi ma Majalisar, sai ya ce ai tun dama rufe Majalisar ya saba ma doka, kuma akwai bukatar a bar sabbin shugabannin Majalisar su zauna su yi ma jama’a aiki.
Da wakilinmu Mustapha ya tambaye shi martaninsa kan ikirarin wanda su ka ce ya zama Tsohon kakakin Majalisar cewa har yanzu shi ne Kakaki saboda Kotu ta haramta tsige shi, sai ya ce ai an zabe shi ne don ya zama dan Majalisa amma ba don ya zama Kakaki ba.
Game da rade-radin cewa Majalisar na bin gwamnatin ta Naija wasu makudan kudaden gudanar da aiki, sai Honorabul Bello Agwara ya ce sam ba wai don wani biyan bukata na son rai ya sa su ka tsige tsoffin shugabannin Majalisar ba, sai don rashin bin ka’ida.
Mustapha Batsari ya ce Kakakin da aka ce an tsige, Hon. Adamu Usuman, bai halarci zaman ba, don haka ya yi kokarin jin ta bakinsa to amma ba a dace ba.
Ya ce a yau dinnan Alhamis Kotu za ta fara saurare karar da Honorabul Adamu Usuman ya kai na kalubalantar tsige shi da aka ce an yi.
Your browser doesn’t support HTML5