‘Yan Sanda Sun Gargadi Masu Shirin "Hambarar" Da Gwamnatin Najeriya

'Yan sandan Najeriya yayin da suke bakin aiki

“Rundunar ‘yan sandan, tana gargadi ga masu shirya wannan zanga zanga da masu marawa kungiyar Global Coalition for Security and Democracy baya, da su yi watsi da wannan gangami da suka shirya.”

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta yi gargadi ga masu shirin ta da zaune tsaye a ranar Litinin mai zuwa inda suke kiran ‘yan Najeriya su fito domin yin zanga zangar neman sauyi a birnin Abuja.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta bayyana hakan ne, a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda take cewa, aiwatar da wannan gangami daidai yake da “cin amanar kasa da aikata ayyukan ta’addanci.”

“An ja hankalin rundunar ‘yan sanda Najeriya kan wani hoton bidiyo da ya karade shafin sada zumunta, wanda wata kungiyar mai suna “Global Coalition for Security and Democracy da sauransu, suke zuga ‘yan Najeriya na ciki da waje, da su shiga wata zanga zanga ta juyin-juya-hali a ranar 5 ga watan Agusta, 2019, da nufin sauya gwamnati.” Sanarwa ta bayyana.

Sanarwar ta kara da cewa, “duk da cewa ‘yan Najeriya na da damar yin zanga zangar, rundunar ‘yan sanda na so ta bayyana cewa, babu hurumin da za a mayar da wannan zanga zanga ta zama ta ta da tarzoma da tilastawa wata gwamnati ta sauka – wanda wannan shi ne manufar wannan zanga zanga.”

“Ba za mu tsaya mu zura ido muna kallo wata kungiya ko wasu su ta da husuma a kasa ba.” In ji sanarwar.

“Rundunar ‘yan sandan, tana gargadi ga masu shirya wannan zanga zanga da masu marawa kungiyar Global Coalition for Security and Democracy baya, da su yi watsi da wannan gangami da suka shirya.”