'Yan Sanda Sun Ceto 'Yar Watanni 15 Daga Barayin Mutane

Kwamishina ‘yan sandan jihar Abia, Mr. Leye Oyebade, yace jami’an rundunar ‘yan Sandan jihar, sun ceto wata yarinya yar watanni goma sha biyar da aka sace ta dake hannun mahaifiyarta.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake yiwa ‘yan jarida bayyani irin ci gaban da rundunar ta samu, ya kuma ce ranar litini aka sace yarinyar a Umuahia, kuma aka gano ta.

Mr.Oyebade, ya ce wadanda ake zargin Lawan Nuhu da Lawal Ahmed, sun sace yarinyar ce bayan da suka bugar da mahaifiyar ta Mrs. Chioma Chijindu, da kayan sa maye.a gidan da suke zauna mai lambar 8, layin Ohafia, a Umuahia.

Su dai wadannan mutane da ake zargi an samesu da mota kira Peugeot 307, mai lambar AZ 166 KWL da tsabar kudi Naira 170,000, kuma sun tabbatar da cewa sun bugar da mahaifiyar yarinyar.

Kwamishinan ya gargadi iyaye dasu sa ido akan harkokin makwabtansu da kuma baki a unguwaninsu.