Tun farko dai an sace mutane a yankin Biaji da ke daf da babbar unguwar Kubwa, wadda titin dogo na Abuja zuwa Kaduna ya ratsa ta yankin. A ranar Juma’a ne wasu mutanen da ba san ko su waye ba, suka sace mutane tara da su ka hada da mata da kananan yara.
Jami’ar labarun rundunar Josephine Adeh, ta musanta labarin cewa an sace mutanen a Kubwa. Adeh ta kara da cewa a halin yanzu rundunar ba za ta fadi halin da a ke ciki na binciken mutanen ba, don kaucewa matsala da za ta iya shafar binciken.
Ya zuwa hada wannan rahotan alamu na nuna cewa har yanzu ba a kai ga gano ko mutum guda ba.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da Sashen Hausa cewa ‘yan bindiga kimain 20 ne su ka shiga rukunin gidajen unguwar, inda su ka yi ta barin wuta da kwacewa mutane kaya masu daraja bayan nan su ka dauke mutane tara.
Josephine ta ce da jin labarin sun garzaya don ceto mutanen da kuma har yanzu aikin da su ke yi kenan.
Saminu Azare, wani mazaunin Kubwa ne da ke daf da yankin ya baiyana rashin mamaki ga sace mutanen a yankin ganin yanda ya ke makwabtaka da dazuka da layin dogo.
Hakika irin wannan yanayi kan jefa fargaba a zuciyar mazauna Abuja, don yadda abubuwan dake faruwa a cikin dazuka yanzu ya shigo gari.
Saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5