‘Yan sanda a arewacin Nijeriya na binciken fashe-fashen bama-baman da su ka tarwatsa wata mashaya a barikin sojoji da yammacin Lahadi, da su ka yi sanadin mutuwar a kalla mutane 10.
Babu wanda ya dau alhakin kai hare-haren uku, da su ka abku a birnin Bauchi ‘yan awoyi kadan bayan rantsar da shugaba Goodluck Jonathan a babban birnin kasar, Abuja.
Ran Lahadi ‘yan sanda sun ce adadin wadanda su ka halaka sun kai 10 to amman wasu jam’an sun ce adadin na ma iya karuwa. Akalla dai mutane 25 ne su ka sami raunuka sanadiyyar tashin bama-baman.
Har ilayau dai ‘yan sanda na binciken tashe-tashen bama-bamai a wasu wurare biyu a cikin birnin Zazzau. Wata fashewa a wata mashaya ran Lahadi ta raunata mutane biyu. Akwai wata fashewar kuma jiya Litini a Zariya. Babu wani cikakken bayanin ko akwai wanda abin ya rutsa das hi.
Shugaba Jonathan dai na fuskantar kalubalen hada kan kasar da ke fama da tashe-tashen hankulan siyasa da bangaranci.
Sama da mutane 800 ne dai su ka hallaka a tashen hankalin day a biyo bayan zabe bayan da aka ayyana Mr. Jonathan a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Afirilu.