Yanzu haka harkokin sufuri da na kasuwanci sun tsaya cik a jahar Taraba bayan zanga-zangar da direbobi suka yi, da ta hada da katse hanyar zuwa Jalingo, sakamakon karya wani direba da wasu ‘yan sanda su ka yi saboda wai ya ki ba su na goro.
Yanzu haka direbobi sun katse hanyar zuwa hedikwatar jahar Taraba, wato Jalingo, bayan karya direban babbar mota da ‘yan sandan su ka yi, a shingen duba ababen hawa da suka kafa a garin Jimlari, lamarin da yanzu ya tsaida harkoki cak, kamar yadda ganau suka tabbatar.
Sadik A. Liman da ke zama sakataren kungiyar manyan motocin haya ta NARTO a jahar Taraba, ya bayyana abubuwan da ke faruwa na yadda ake tatsar su.
To saidai, da aka tuntube shi, kakakin Rundunar ‘yan sandan jahar ta Taraba, ASP Othman Abubakar, ya ce za a magance al’amarin.
Ba dai wannan ne karon farko ba da ake zargin jami’an tsaro da tursasa wa matafiya da direbobi ba, lamarin da kan jawo katse hanya.
Ga dai wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz da rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5