'Yan Sanda A Najeriya Sun Kama Wani Jigo A Kungiyar Boko Haram

Umar Abdulmalik

A wata nasara wadda, ko shakka babu, za ta kara ma 'yan Najeriya karfin gwiwa a yakin da jami'an tsaron kasar ke yi da 'yan Boko Haram, 'yan sandan kasar sun ba da sanarwar kama wani gagarabadan kungiyar Boko Haram.

Shelkwatar Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta tabbatar da cewa shi wannan babban kwamanda na mayakan Boko Haram mai suna Umar Abdulmalik, shi ya jagoranci hare haren Bom da aka kai a unguwar Nyaya, da garin Kuje dukkanninsu dake birnin Abuja a shekara ta 2015.

'Yan sandan su ka ce wannan kwamandan, shi da wasu mayakansa guda bakwai, su suka bindige 'yan sandan nan bakwai a unguwar Galadimawa, da karin wasu 'yan sanda biyu, sai wani dan sanda a Lugbe, duk a Abuja.

Kamar yadda 'yan sandan su ka yi karin haske, shi wannan kwamandan, da bakinsa ya shaida masu cewa, shi ya jagoranci fasa gidan Yari na Minna a jihar Naija, inda Fursunoni kimanin 219 suka tsere, ciki har da 'yan kungiyarsa.

Bugudakari shine kuma ya jagoranci fashi da makami a bankunan jihohin Edio da Ondo, satar mutane da na kashe kashe a jihar Kogi.

Mai sharhi kan sha'anin tsaro Mohammed I. Usman, ya ce wannan babban kamu da 'yan sandan su ka yi babbar nasara ce ga Gwamnati, da al'ummar Najeriya, musamman ganin yanzu kwanaki kadan su ka rage a gudanar da babban zabe na kasa.

Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Sanda A Najeriya Sun Kama Jigo A Kungiyar Boko Haram 2'40"