'Yan Sanda A Kasar Ghana Sun Gano Wuraren Da Ka Iya Fuskantar Rikici A Lokacin Zabe

Yan sanda a Ghana sunce sun gano wasu wurare da suka kai 5,000 dake buktar kulawa, inda ake ganin za a iya samun tashin tarzoma kafin babban kasar na ran 7 ga watan Desimbar wannan shekara, kuma yan sanda sun fara daukar matakai na magance wannan rigimar da ake fargabar zata iya tashi.

Kakakin ma’aikatar yan sandan Ghana Cephas Arthur yace rundunar ‘yan sanda na da alhakin da iko da kundin tsarin mulkin kasar ya bata na tabbatar da zaman lafiyar jama’a a lokacin wadannan zabuka na shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki da kuma na kananan hukumomi da za’ayi.

Cephas Arthur ya bada wadannan alkalumman wurare 5,000 da za a iya samu rigingimu a fadin kasar baki daya ne, biyo bayan wani kashedi da hukumar zaben kasar ta yi cewa akwai yiyuwar barkewar tashin hankali a kashi 30 cikin dari na mazubun kasar.